in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu ta sake musanta batun ba da goro don samun damar karbar bakuncin gasar FIFA
2015-06-04 09:57:16 cri

Mahukunta a Afirka ta Kudu, sun sake jaddada matsayarsu ta kin amincewa da zargin da ake musu, na ba da toshiyar baki domin samun damar karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, wadda hukumar FIFA ta gudanar a shekarar 2010.

Da yake karin haske game da wannan batu, ministan wasannin kasar Fikile Mbalula, ya ce, dala miliyan 10 da ake zargin kasarsa ta baiwa hukumomin kwallon kafar yankunan arewaci da tsakiyar Amurka da Caribbean, ba toshiyar baki ba ce. A cewarsa, an baiwa hukumar wasannin yankunan wato Concacaf wadannan kudade ne, a matsayin gudummawar raya harkokin wasanni, wanda kuma ko shakka babu 'ya'yan nahiyar Afirka mazauna yankuna su ma za su ci gajiyar tallafin.

Mr. Mbalula ya kara da cewa, nahiyar Afirka ta ci gajiyar tallafin kudin gudanar da gasar ta 2010, inda aka baiwa Afirka ta Kudun kudi har dala miliyan 70, hakan ne kuma ya sanya kasar ware dala miliyan 10, domin tallafawa wancan yanki karkashin hukumar ta Concacaf.

Ministan wasannin ya kuma ce, kasar sa na dakon shaidun da mahukuntan kasar Amurka za su gabatar, wadanda za su tabbatar da zargin da ake yiwa Afirka ta Kudun, don gane da aikata laifin cin hanci ko ba da rashawa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China