in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha za ta ciyo bashin dala miliyan 300 daga bankin duniya don shirin inganta rayuwar jama'a
2016-01-13 11:01:40 cri

Kasar Habasha ta rattaba hannun na amincewa da karbar bashin dalar Amurka miliyan 300 daga bankin duniya domin aiwatar da shirin ingata rayuwar jama'ar kasar wacce ke shiyyar gabashin Afrika.

Abdulaziz Mohamed, shi ne ministan kudi da tattalin arziki na kasar, wanda ya rattaba hannu a madadin kasar, yayin da Carolyn Turk, jami'ar bankin duniya a kasar Habasha ta sanya hannu a madadin bankin duniyar wanda aka gudanar a Addis Ababa, babban birnin kasar.

Shirin wanda za'a aiwatar da shi cikin shekaru biyar, zai lashe kudin da ya kai dalar Amurka miliyan 450, wanda za'a aiwatar da shi da nufin inganta hanyoyin samun kudaden shiga ga magidanta masu karamin karfe dake zaune a biranen kasar ta Habasha.

Wannan shiri ya hada da musayar kudade da ba da tallafin kwarewa domin al'umma su samu damar inganta rayuwar su, da kara bunkasa ci gaban masana'antu, ta yadda za su gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.

Abdulaziz, ya bayayya cewar, shirin ya samu karbuwa a kasar ne, bisa la'akari da irin nasarorin da ya samar a yankunan karkara tun daga shekarar 2005.

Ministan ya kara da cewar, gwamnatin Habasha za ta ba da gudumawar dala miliyan 150 wanda adadin kudin baki daya ya tasamma dalar Amurka miliyan 450.

A kashin farko na wannan shirin, mutane dubu 600 daga biranen kasar 11 ne za su amfana da shirin.

Jami'ar bankin duniyar ta ce, wannan shiri na UPSNP, shi ne irinsa na farko da aka taba aiwatarwa a nahiyar Afrika, sannan ta kara da cewar, shirin zai taimakawa gwamnatin kasar wajen nasarar dabarunta na bunkasa ci gaban kasar da samun kyakkyawar makoma ta fuskar ci gaban kasar.

Carolyn Turk, ta kara da cewar, shirin zai taimaka wajen cimma muradin kasar a shirinta na bunkasa ci gaban Habasha karo na biyu wato GTP II a takaice, shiri ne wanda ke da aniyar inganta rayuwar jama'a masu karamin karfi da marasa galihu don samar musu hanyoyin kudaden shiga.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China