in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar asusun IMF ta isa Najeriya don tattauna ci gaban tattalin arziki
2016-01-05 09:28:07 cri

Babbar daraktar asusun ba da lamuni na IMF Christine Lagarde, ta isa birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya, domin tattauna da mahukuntan kasar game da batutuwan da suka shafi ci gaban tattalin arziki.

Lagarde, wadda ta samu tarbar minista a ma'aikatar kudin kasar Kemi Adeosun, da gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele a jiya Litinin, za ta shafe kwanaki hudu tana zantawa da sassan masu ruwa da tsaki a fannin ci gaban kasar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, Largarde za ta gana da shugaba Muhammadu Buhari, tare da tawagar masana a fannin tattalin arzikin Najeriya. Kana za ta tattauna da 'yan majalissun dokokin kasar, da 'yan kasuwa, da wakilan mata da dai sauran su.

Gabanin fara wannan ziyara, jami'ar asusun na IMF ta shaidawa manema labarai fatan ta, inda ta ce, tana da burin ganawa da masu ruwa da tsaki a Najeriya, duba da yadda suka jajirce wajen ganin sun bunkasa yanayin cinikayya da zuba jari a kasar, tare da samar da damar inganta ci gaban fannoni masu zaman kan su, a daidai gabar da farashin mai ke karyewa a kasuwannin duniya.

Baya ga Najeriya, Lagarde za ta gudanar da ziyarar aiki ta yini biyu a kasar Kamaru.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China