Wani jami'in gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ya ce, za'a aiwatar da sabbin dokoki da suka shafi neman takardun izinin shiga kasar wato Visa.
Babban daraktan hukumar kula da al'amurran cikin gida na kasar Mkuseli Apleni, ya ce, sabbin tsare tsaren za su fara aiki ne nan da watanni 3 masu zuwa, wadanda suka hada da na tantance manyan kamfanonin yawon bude ido na kasashen Sin, da Indiya, da kuma Rasha, wanda sabbin matakan za su hada da kara wa'adi ga masu sha'awar ziyartar wadancan kasashen.
Da yake karin haske ga masu ruwa da tsaki kan al'amurran shigi da fici na kasar a birnin Johannesburg, Apleni, ya ce, nan da watanni 3, kasar za ta fara aikin gwajin daukar hoton 'yan yatsu ga mutane a manyan filayen jiragen saman kasar 3.
Tsakanin watanni 3 zuwa shekara guda, kasar za ta aiwatar da sauran matakan da suka shafi tafiye tafiye, da suka hada da kara cibiyoyin ba da takardun izinin zuwa kasashen Sin da Indiya da kuma Zimbabwe.(Ahmad Fagam)