Shuagabn kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika ya aike da sakon taya murna ga takwaransa na Tunisia Caid Beji Essebsi bayan da kasarsa ta samu kyautar Nobel ta zaman lafiya da aka baiwa kwamitin sassanta 'yan kasa a ranar Jumma'ar da ta gabata.
A albarkacin ba da wannan kyautar Nobel ta zaman lafiya ta shekarar 2015 ga kwamitin, da ya jagoranci shawarwarin sassanta 'yan kasar Tunisia, a madadin sunana, gwamnati da al'ummar Aljeriya, ina aike muku da sakon taya murna game da wannan karramawa, in ji shugaba Boutefilka a cikin wata wasika da kamfanin dillancin labarai na APS ya rawaito a ranar Lahadi.
Kwamitin sassanta 'yan kasa, wani gungu ne dake kunshe da kungiyar kwadago ta UGTT, kungiyar 'yan kasuwa da masu masana'antu ta Tunisia, kungiyar kare hakkin dan adam da kuma kungiyar alkalai ta kasa.
Aikin wannan kwamiti ya taimaka wa Tunisia kaucewa rikici tsakanin masu kishin islama da kuma masu adawa da ya yi barazanar tura kasar cikin tashin hankali. (Maman Ada)