in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Aljeriya sun halaka 'yan tawaye sama da 100 a wannan shekara
2015-12-28 09:36:49 cri

Ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya ta bayyana a cikin rahotonta na shekara-shekara cewa, a shekarar 2015 da muke ciki, dakarun kasar sun kashe 'yan tawayen da yawansu ya kai 109 baya ga wasu 36 da suka kama.

Rahoton ya kara da cewa, dakarun sun kuma yi nasarar kwace wasu abubuwan fashewa 18, da bama-bamai 182 da kuma nakiyoyi 123. Bugu da kari dakarun da ke yaki da ta'addanci sun yi nasarar kwace manyan bindigogi kirar Kalashnikov 105, da kananan bindigogi masu sarrafa kansu 21, da albarusai 237, da wasu bindigogi sanfurin FMPK 23, da makaman harbo roka 13 da kuma makamai masu linzami 5. Wannan a cewar rahoton, wani mataki ne na yaki da ayyukan ta'addanci a fadin kasar.

A shekarun 1990 ne yakin basasa ya balle a kasar ta Aljeriya tsakanin dakarun tsaro da 'yan tawaye masu kishin Islama, bayan da sojoji suka soke zabukan majalisun dokoki a shekarar 1992, zaben da jam'iyyar FIS da aka rushe ta dauko hanyar lashe shi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China