Hukumar zaben kasar Tanzaniya ta ayyana 'dan takarar jam'iyyar CCM mai mulki John Pombe Magafuli a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.
Magafuki wanda ya cika shekaru 56 a jiya, shi ne zai kasance shugaban Tanzaniya na biyar bayan da gaji shugaba Jakaye Kikwete wanda ya kammala wa'adin shugabancinsa na biyu na shekaru biyar.
Magafuli dai ya samu kashi 58 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben, yayin da abokin hamayyarsa tsohon firaministan kasar Edward Lowassa na jam'iyyar adawa ta Chadema ya samu kusan kashi 40 cikin 100. Ko da yake Lowassa ya nuna shakku game da sakamakon da hukumar zaben kasar ta bayyana.
Rahotanni na nuna cewa, akwai fargabar magoyan bayan 'yan adawa za su gudanar da zanga-zanga, amma 'yan sanda sun bayyana cewa, al'amari na tafiya kamar yadda aka saba a kasar.
Sai dai masu sa-ido na kasa da kasa a zaben sun bayyana cewa, zaben ya gudana cikin lumana.
Sama da mutane miliyan 22 ne suka fito kada kuri'a don zaben sabon shugaban kasa da 'yan majalisun dokoki a zaben na ranar Lahadi. (Ibrahim)