in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan takarar jam'iyya mai mulki ne ke kan gaba a sakamakon farko na zaben Tanzaniya
2015-10-27 10:49:19 cri

A sakamakon farko da hukumar zaben kasar Tanzaniya ta fitar a Litinin din nan, ya nuna cewar, 'dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi CCM mai mulkin kasar Dr John Magufuli ne ke kan gaba a runfunan zabe 9 daga cikin adadin rumfuna 264 da ke kasar.

Shugaban hukumar zaben kasar Judge Damian Lubuva, ya fada a taron manema labaru a birnin Darussalam cewar, ya zuwa yanzu, hukumar zaben kasar ta kammala kidaya sakamakon zaben mazabu 4 daga cikin mazabu 13 dake kasar, inda 'dan takarar jam'iyyar adawa ta CHADEMA Edward Lowassa ne ya lashe zaben a mazabun.

Kuma ya tabbatar da cewar, da zarar hukumar zaben kasar ta kammala tattara sakamakon zaben, za ta sanar da shi.

Mai magana da yawun jam'iyyar CCM mai mulkin kasar January Makamba, ya ce, kawo yanzu, jam'iyyar tasu ta lashe zaben a rumfunan zabe 176 daga cikin rumfunan zabe 264 dake fadin kasar.

Makamba, ya kara da cewar, a yanzu haka sun samu nasara a mazabu 11 wadanda da farkon 'yan adawa ne ke kan gaba a mazabun.

Sannan ya bukaci magoya bayansu, da su kwantar da hankali har zuwa lokacin da hukumar zaben kasar za ta sanar da sakamakon zaben na karshe.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China