in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi allah wadai da harin da aka kai a Chadi
2015-07-13 10:09:26 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi kakkausar suka kan harin kunar bakin waken da aka kai babbar kasuwar N'Djamena, babban birnin kasar Chadi.

Mr Ban wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun kakakinsa, ya sake nanata muhimmancin aikin tare tsakanin kasashe na kara daukar matakan yaki da ayyukan ta'addanci kamar yadda dokokin jin kai da kare hakkin dan-adam da na 'yan gudun hijira na kasa da kasa suka tanada.

Harin na ranar Asabar dai ya sabbaba mutuwar mutane 16, kana wasu 80 suka jikkata. Wani jami'in yankin ya bayyana cewa, 'dan kunar bakin waken ya yi shigar mata ne inda ya tayar da bam din da ke jikinsa lokacin da 'yan sanda suka yi kokarin kama shi a mashigar babbar kasuwar daga kudu.

Ko da a ranar 15 ga watan Yuni ma an kai wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake a birnin na N'Djamena, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 38, kana wasu sama da 100 suka jikkata.

Gwamnatin Chadi dai na zargin kungiyar Boko Haram da kai wadannan hare-hare.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China