in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An jinjinawa matakin gurfanar da tsohon shugaban Chadi gaban kuliya
2015-07-21 10:36:49 cri

Babban kwamishinan MDD mai lura da harkokin kare hakkin bil adama Zeid Ra'ad Al Hussein, ya jinjinawa kudurin gurfanar da tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre gaban kuliya.

Mr Habre dai zai amsa tuhuma ne kan zarge-zargen aikata laifukan yaki, da kisan kiyashi, tare da keta hakkokin bil adama lokacin da yake mulki, tsakanin shekarun 1982 zuwa 1990. Zai kuma gurfana ne a gaban wata kotun, musamman da aka kafa domin gudanar da shari'ar tasa a kasar Senegal.

A cewar Zeid, gurfanar da tsohon shugaban kasar ta Chadi ya nuna cewa, babu wani shugaba da zai tsallake hukunci komin tsahon lokaci, muddin dai ya aikata laifuka da suka sabawa doka, a lokacin da yake kan karagar mulki.

Tun dai barinsa karagar mulki shekaru 25 da suka gabata, tsohon shugaban na Chadi ke samun mafaka a kasar Senegal. A kuma ranar 22 ga watan Agustan shekara ta 2012 ne mahukuntan kasar Senegal, da wakilan kungiyar hadin kan Afirka ta AU suka amince da kafa kotun musamman, wadda za ta saurari korafin da aka gabatar game da yadda Hissene Habre, ya keta dokokin kasarsa, da ma na kasa da kasa, lokacin da yake kan karagar mulki. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China