in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Maganin malariya da 'yar kasar Sin ta kirkiro yana ceton jama'ar Ghana
2015-10-15 10:25:17 cri

Maganin Artemisinin, na malariya wato zazzabin cizon sauro da wadda ta samo lambar yabo ta Nobel kuma 'yar kasar Sin Tu Youyou da sauran abokan aikinta suka kirkiro da shi ya zama wani abin da zai ceci al'ummar kasar Ghana, in ji wassu jami'an hada magunguna na kasar.

Arnold Ferdinand, wani jami'in hada magunguna a kusa da Accra, babban birnin kasar ya ce, an samu matukar ci gaba wajen magance cutar ta zazzabin cizon sauro a Ghana tun bayan da wannan magani ya bayyana. Ya yi bayanin cewa, mutanen dake fama da cutar suna samun sauki cikin 'dan kankanin lokaci bayan an ba su maganin.

Kwabena Bimpong shi ma wani babban jami'in hada magunguna, ya bayyana maganin Artemisinin a matsayin mai ceton jama'a a kasar. Ya ce, malariya ta zama babban abin da ke kisan jama'a kwarai a yammacin nahiyar Afrika wadda kididdiga ta nuna cewa, a kalla mutane 4,000 ke mutuwa a duk shekara. Bimpong ya ce, a samu irin maganin da yake matukar aiki a Ghana da ma nahiyar Afrika baki daya abin a yaba ne.

Babbar likita a bangaren hada magungunan gargajiya, 'yar kasar Sin Tu Youyou ta samu kyautar lambar Nobel na wannan shekarar a bangaren likitanci dalilin aikinta na samo wannan magani da ya ceci rayukan mutane da dama.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China