in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran za ta gudanar da atisayen sojojin ruwa a tekun Indiya
2016-01-11 10:12:05 cri

Nan ba da dadewa ba ne kasar Iran za ta gudanar da wani atisayen sojojin ruwa a yankunan arewacin tekun Indiya.

Babban kwamandan ruwa na kasar Iran Gholamreza Khadem Bigham ya sanar da cewa, za a gudanar da atisayen mai taken "Velayat 94" ne a ranar 20 ga watan Janairun wannan shekara.

Manufar wannan atisaye, a cewar babban kwamandan, ita ce, auna karfi da kuma ingancin na'urorin mayakan ruwan kasar ta Iran.

Ya kuma bayyana cewa, kasancewar kasar Iran a ruwayen kasa da kasa tare da gudanar da atisayen sojojin ruwa, ya nuna yadda jamhuriyar musulunci ta Iran ke kara karfi da kimtsawa, matakin da kwamandan ya bayyana a matsayin muhimmiyar dabara.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China