in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somaliya ta katse huldar diflomasiya da Iran
2016-01-08 09:20:42 cri

A jiya ne gwamnatin kasar Somaliya ta sanar da katse huldar diflomasiya da kasar Iran, sakamakon harin da wasu Iraniyawa masu zanza-zanga suka kai kan ofishin jakadancin kasar Saudiya da ke birnin Tehran.

Ma'aikatar harkokin waje da inganta harkokin zuba jari ta kasar Somaliya ta kira jami'in ofishin jakadancin Jamhuriyar musulunci ta Iran da ke Mogadishu domin sanar da shi shawarar da ta yanke ta katse huldar jakadanci da Iran din.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Somaliyan ta fitar ta kuma bayyana cewa, kasar ta dauki wannan mataki ne bayan dogon nazari kan yadda kasar Iran din ke ci gaba da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar ta Somaliya.

Matakin da Somaliya ta dauka na zuwa ne tun bayan da kasar Saudiya ta yanke huldar jakadanci da Iran a ranar 3 ga watan Janairu, bayan da wasu masu bore suka kona ofishin jakadancin Saudiya da ke Tehran da kuma karamin ofishin jakadancinta a Mashhad da ke arewa maso gabashin kasar, don nuna bacin ransu game da hukuncin kisan da mahukuntan Saudiya suka yanke kan wani malamin 'yan shi'a Sheikh Nimr al-Nimr.

Somaliya dai ita ce kasa ta farko a yankin arewacin Afirka da ta yanke huldar diflomasiya da Iran bayan kasar Djibouti, wadda ita ma ta sanar da katse hulda da kasar ta Iran a ranar Laraba, yayin da Qatar ta dawo da nata jakadan zuwa gida.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China