in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kara kyautata tsarin inshorar kiwon lafiyar dukkan al'ummominta
2016-01-09 13:06:43 cri
A yayin taron aikin kiwon lafiya da shirin haihuwa na shekarar 2016 da aka shirya a kwanan baya, madam Li Bin, minister kula da aikin kiwon lafiya da shirin haihuwa ta kasar ta bayyana cewa, a shekara ta 2016, kasar Sin za ta hanzarta yin gyare-gyare kan tsarin kiwon lafiya da hanyar samar da magunguna, kana za ta kara yin gyare-gyare kan hanyoyin gudanar da asibitocin gwamnati. Haka kuman za ta kara kyautata tsarin inshorar kiwon lafiyar dukkan al'ummominta, tare da ba da aikin jinya bisa matakai daban daban. Bugu da kari, za ta dauki matakai na a zo a gani wajen aiwatar da manufofin haihuwar yara biyu a duk kasar gaba daya. Dadin dadawa, madam Li ta ce, hukumomin kiwon lafiya za su yi kokarin kyautata ingancin ba da jinya ga jama'a.

Bisa bayanin da aka bayar, an ce, a cikin shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta dauki kwararan matakai da dama wajen yin gyare-gyare kan harkokin kiwon lafiya da ba da jinya. Sakamakon haka, yawan kiyasin tsawon rayuwar jama'a a duniya da yawan mutuwar mata masu juna biyu da yawan mutuwar sabbin jarirai da wasu sauran muhimman adadin dake da nasaba da lafiyar jama'a sun cimma burin da gwamnatin kasar Sin ta tsara yau da shekaru biyar da suka gabata, da MDD ta tsara a shirin neman ci gaba a shekarar ta 2000, matsayin lafiya da Sinawa suke dauka ya kai kusan daidai da na kasashe masu arziki. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China