in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Platini ya janye daga takarar shugabancin hukumar FIFA
2016-01-08 11:31:57 cri
Shugaban hukumar kwallon kafar Turai Michel Platini, ya sanar da janyewa daga batun takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA. Platini ya bayyana hakan ne a ranar 7 ga wata, matakin da ya ce ya dauke shi ne domin kare mutuncinsa.

A watan Disamba na shekarar 2015 ne kwamitin ladabtarwa na hukumar FIFA ya sanar da yanke hukuncin dakatar da Sepp Blatter, da Michel Platini daga dukkanin harkokin da suka shafi wasan kwallon kafa har tsawon shekaru 8. Ga alama dai Platini ba zai iya samun amincewar 'yan kwamitin zaben hukumar FIFA kafin nan da ranar 26 ga watan nan na Janairun bana, don haka ba zai samu dama ta shiga takara a zaben dake tafe a ranar 26 ga watan Febrairu ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China