in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a shiga zagaye na biyu na babban zabe a CAR
2016-01-08 09:48:02 cri

Al'ummar janhuriyar Afirka ta tsakiya CAR za su kada kuri'u a zagaye na biyu, na zaben shugaban kasa a ranar 31 ga watan nan na Janairu. Rahotanni na cewa, sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 30 ga watan Disamba, ya nuna babu wani 'dan takara daya tilo da ya lashe zaben.

Kimanin 'yan kasar miliyan 1 da dubu dari 9 ne suka kada kuri'un su a zaben na ranar 30 ga watan Disamba, a mazabu 5,996 dake sassan kasar daban daban, domin zabar shugaban kasa, da kuma 'yan majalissun dokokin kasar 140.

Idan dai ba a manta ba janhuriyar Afirka ta tsakiya ta tsunduma yakin basasa ne a ranar 10 ga watan Disambar shekarar 2012, lokacin da dakarun Seleka da na gwamanatin kasar suka shiga dauki ba dadi da juna. Sakamakon hakan ne kuma Seleka ta amshe mulkin kasar daga hannun shugaba Francois Bozize a cikin watan Maris na shekarar 2013 inda Michel Djotodia ya ayyana kan sa a matsayin shugaba.

A kuma shekarar 2014 yawaitar tashe-tashen hankula suka tursasa Djotodia sauka daga karagar mulkin kasar, kana Catherine Samba-Panza ta zamo shugabar rikon kwarya.

Ana dai sa ran zaben da ake shirin kammalawa zai kawo karshen halin rashin tabbas da janhuriyar Afirka ta tsakiyar ke fuskanta a halin yanzu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China