in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hery Rajaonarimampianina na kan gaba a zaben shugaban Madagascar
2013-12-23 10:47:44 cri

Dan takara Hery Rajaonarimampianina ne kan gaba bisa ga sakamakon kidaya na wucin gadi da aka samu daga rumfunan zabe 3047 da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (CENIT) ta gabatar a ranar Lahadi.

Bisa sakamakon wadannan rumfuna 3047 da aka gabatar, hukumar CENIT ta kidaya masu zabe 1761678 daga cikinsu 877040 sun kada kuri'unsu, lamarin da ya ba da kashi 95,56 cikin 100 na adadin da ake bukata.

Hery Rajaonarimampianina da ya samu goyon bayan shugaban mulkin wucin gadi Andry Rajeolina ya samu kashi 53,63 cikin 100 a yayin da abokin takararsa, Jean Louis Robinson da ya samu goyon bayan tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana da ya samu mafakar siyasa a kasar Afrika ta Kudu ya samu kashi 46,37 cikin 100.

Bisa ga wannan sakamako na wucin gadi, adadin mutanen da suka halarci zaben ya kai kashi 49.78 cikin 100 a yayin wannan zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka shirya tare da na 'yan majalisun dokoki a ranar Jumma'a. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China