Mahukunta a kasar Madagaska, sun haramta gudanar da tarukan jama'a, gabanin ayyana sakamakon zagayen farko na babban zaben kasar.
Da yake karin haske don gane da daukar wannan mataki, mataimakin babban jami'in rundunar tsaron kasar kanar Rakotonirina Lala, ya ce, za a cafke dukkanin wani mutum da ya shirya wani taron jama'a ba tare da neman izini ba. Lala ya kara da cewa, jami'an tsaro ba za su aminci dukkanin wani mataki da ka iya haddasa barkewar tarzoma ba. Wannan mataki dai na zuwa ne biyowa bayan rade-radin da ake yi cewa, wasu na shirin ta da hargitsi, da zarar an bayyana sakamakon zaben da al'ummar kasar suka kada a ranar 25 ga watan Oktobar da ya gabata. Ana dai sa ran wata kotun kasar ta musamman ce za ta bayyana sakamakon zaben a Juma'ar nan.
Sakamakon da hukumar zaben kasar ta bayyana ran 8 ga watan Nuwambar da ya shude dai ya nuna cewa, Jean Louis Robinson, wanda ya samu goyon bayan tsohon shugaba Marc Ravalomanana ne ke kan gaba da kaso 21.44 bisa dari na kuri'un da aka kada. Sai kuma Hery Rajaonarimampianina, wanda ke da goyon bayan shugaban rikon kwaryar kasar Andry Rajoelina, a matsayi na biyu, da kuri'u kaso 15.68 bisa dari.
Bisa kuma tsarin mulkin kasar, 'yan takarar biyu dake kan gaba, za su shiga zabe a zagaye na biyu, wanda ake fatan gudanarwa a ranar 20 ga watan Disambar dake tafe. (Saminu)