Kungiya mai tsattsauran ra'ayi ta IS ta sanar da daukar alhakin kai farmakin boma-boman kunar bakin wake a wani masallacin dake kudu maso yammacin kasar Saudiyya a jiya Alhamis, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 15, a yayin da mutane 7 suka ji rauni.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Saudiyya ta ce, a tsakar ranar Alhamis, an kai hari kan wani masallacin da ke karkashin wata rundunar 'yan sanda ta kasar Saudiyya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan sanda 10 da kuma ma'aikata 3, a yayin da mutane 9 suka ji rauni, kuma 'yan sanda 2 daga cikinsu sun rasu a lokacin da suke karbar jinya.
Bayan fashewar boma-boman, kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai wannan farmaki a kan shafinta na internet, tare da fayyace cewa, za ta kai kuma wasu karin hare-hare a kasashen Larabawa a nan gaba.(Lami)