in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Algeria ya sauya jagoran hukumar leken asiri
2015-09-14 09:43:46 cri

Shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika, ya sauke Manjo Janar Mohamed Mediene, shugaban hukumar leken asirin ta DRS daga mukaminsa.

Rahotanni sun ce, shugaba Bouteflika ya kuma maye gurbin Mediene da Mr. Othmane Tatag, wanda kafin nadinsa daya ne daga mashawartan shugaban kasar, ya kuma taba aiki a hukumar leken asirin kasar.

A cewar shugaban jam'iyyar FLN mai mulkin kasar Amar Saadani, shugaban na Aljeriya na gudanar da ire-iren wadannan sauye sauye kan rundunonin soji, da sauran jami'an tsaron kasar ne, a wani mataki na aiwatar da gyaran fuska ga tsarin gudanar da mulki.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China