in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi gwajin farko bisa layin dogo tsakanin Djibouti da Habasha
2015-08-31 10:37:48 cri

An gudanar a ranar Lahadi da gwajin karko na jirgin kasa bisa sabon layin dogo tsakanin kasashen Djibouti da Habasha, da ya taso daga hanyar jirgin kasa ta Djibouti.

Bikin ya samu halartar ministan sufurin Djibouti Moussa Ahmed Hassan, wanda kuma burin shi ne na ganin yadda aka gudanar da ayyuka har zuwa yanzu.

Kuma wannan ne taragon farko bisa hanyar sa ta zuwa Addis Abeba na sabon jirgin kasa dake jaye da taragogi kusan talatin masu daukar man fetur da babu kome a cikinsu zuwa kasar Habasha. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China