in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani 'dan ta'adda ya tsere daga gidan yarin Nouakchott na Mauritaniya
2016-01-04 10:32:33 cri

Salek Ould Cheikh 'dan kasar Mauritaniya, wanda aka yanke wa hukuncin kisa, dalilin ayyukan ta'addanci, ya tsere daga gidan yarin birnin Nouakchott, inda ake tsare da shi a cikin wani yanayi na rufa ido, da har yanzu ake neman fahimtar wannan lamari.

Wani sakon farautarsa da ake yi da hukumomin gidan yari suka watsa a ranar Lahadi, ya nuna cewa, wanda ya tseren, an haife shi a shekarar 1984 a Atar dake arewacin kasar, kuma ana daukarsa a matsayin wani babban dan ta'adda, wanda kuma aka taba yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2011 bisa wani yunkurin da ya yi na tada bom a birnin Nouakchott, kuma ya tsere ne daga gidan yari a ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2015. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China