in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta amince da tura tawagar sanya ido a zaben shugaban Mauritaniya
2014-06-10 10:27:16 cri

Shugabar kwamitin tarayyar Afrika AU Nkosazana Dlamini-Zuma, ta amince da tura wata tawagar sanya ido ta kungitar AU (AUEOM) a kasar Mauritaniya, game da zaben shugaban kasar da zai gudana a wannan kasa a ranar 21 ga watan Junin shekarar 2014.

A cikin wata sanarwar da aka fitar a ranar Litinin, kungiyar AU ta bayyana cewa, tawagar AUEOM a karkashin jagorancin tsohon faraministan kasar Tunisiya Beju Caid Essebi za ta isa wannan kasa daga ranar 13 zuwa 28 ga watan Juni. Tawagar za ta kunshe mambobi 40 masu sa ido na AU da suka fito daga manyan hukumomin nahiyar Afrika kamar majalisar dokokin Afrika, kungiyoyin kare hakkin dan adam da kungiyoyin fararen hula na Afrika, a cewar wannan sanarwa.

Aikin tawagar AUEOM zai shafi sanya ido kan shirin zaben Mauritaniya, kuma tawagar za ta gudanar da aikinta tare amincewar hukumomi na matakai daban daban na kungiyar AU wajen sanya ido kan zabubuka kamar kundin tsarin demokaradiyya na Afrika, zabubuka da tsarin mulki na gari, sanarwar kungiyar AU da ta OAU kan tsare-tsaren dake tafiyar da zabubuka bisa tushen demokaradiyya a Afrika da sauransu, in ji wannan sanarwar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China