in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NATO ta tattauna game da yanayin da ake ciki a Turkiya
2015-07-29 09:55:12 cri

A jiya ne kungiyar tsaro ta NATO ta kira wani taro na musamman don tattauna yanayin da ake ciki a kasar Turkiya, bayan wani harin ta'addancin da aka kaddamar a kasar.

Babban sakataren kungiyar Jens Stoltenberg ya ce, kungiyar ta gana ne bisa bukatar kasar ta Turkiya kamar yadda dokokin kungiyar suka tanada don nazartar mummunan yanayin da kasar ta tsinci kanta a ciki.

A yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta kira, kungiyar ta yi allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren ta'addancin da aka kai a kasar ta Turkiya. Kungiyar ta kuma mika ta'aziyarta ga gwamnatin Turkiya da kuma iyalan wadanda hare-haren na Suruc, da ma sauran hare-haren da aka kaddamar kan 'yan sanda da jami'an soji suka rutsa da su.

Ya ce, kungiyar ba za ta amince da duk wani nau'in na ayyukan ta'adanci ba. Ta kuma bayyana kudurinta na ci gaba da bin diddigin abubuwan da ke faruwa a yankunan da ke kudu maso gabashin iyakar kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China