in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar da Turkiya sun rattaba hannu kan yarjejeniya domin bunkasa hulda tsakaninsu
2014-03-12 10:46:33 cri

Kasar Turkiya da jamhuriyar kasar Nijar sun sanya hannu a kan wata yarjejeniyar bunkasa hulda tsakanin kasashen biyu a bangarori 6, wadanda suka hada da noma, tsaro, samar da abubuwan more ayuwa, sufuri, kiwon lafiya da makamashi.

A yayin da yake jawabi ga wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da shugaban kasar Turkiya Abdullah Gul, a Ankara, babban birnin kasar Turkiya, shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou ya ce, "babban fatanmu shi ne tabbatar da girka gamayya tare da goyon bayan Turkiyya."

Shugaban ya kara da cewar, a misali, kasar tasa dake Afrika tana bukatar ruwa, a yayin da Turkiya ta yi alkawarin tallafi a bangaren ayyukan noma, domin samar da abinci a Nijar.

Mahamadou Issoufou, shugaban kasar ta Nijar ya jaddada mahimmancin samun moriya daga kwarewar hukumomin tsaro na kasar Turkiya, domin kyautata kwazon 'yan sandan Nijar a musamman a bangaren bincike.

Ya kara da cewar, ministan hakar ma'adinai na Nijar, zai yi aiki da hukumomin Turkiya, musamman a bangaren ma'adinin Uranium.

A nashi bangaren, shugaban kasar Turkiya Abdullah Gul ya ce, Turkiya da Nijar za su yi aiki tare, a bangaren ma'adinai na Nijar, inda ya ba da tabbacin cewar, kamfanonin Turkiya za su taka rawa wajen saka jari a wannan bangaren na ma'adinai. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China