in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uganda da Kenya na cikin shirin ko ta kwana bayan harin ta'addancin Paris
2015-11-16 10:12:52 cri

Bayan hare haren ta'addancin da suka abku a ranar Jumma'a a birnin Paris, Uganda da Kenya, kasashe biyu da suka taba fama da hare haren ta'addanci, sun kara tsaurara matakan tsaro.

Fred Enanga, kakakin 'yan sandan Uganda, ya bayyana cewa, an kara jibge 'yan sanda, sojoji da jami'an leken asiri a Kampala, hedkwatar kasar Uganda, har ma zuwa yankunan iyakokin kasar.

Ba za mu dauki abubuwan da suka faru a birnin Paris da sassauci ba. Mun kara karin matakan tsaro, ta yadda za mu kare al'ummar Uganda daga barazanar ta'addanci. Irin wadannan matakan tsaro da muka dauka a baya sun taimaka sosai wajen murkushe ayyukan ta'addanci, in ji mista Enanga.

A kasar Kenya, mai makwabtaka da Somaliya, 'yan sanda sun karfafa matakan tsaro bayan hare haren ta'addanci a Paris. Sufeto janar na 'yan sanda, Joseph Boinett ya bayyana cewa, karfafa shirin ko ta kwana na da muhimmanci wajen yin rigakafin hare haren ta'addanci. Mista Boinett da bai bayyana matakan tsaron ba, ya jaddada cewa, akwai barazanar ta'addanci sosai a Kenya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China