Yan tawayen kasar Uganda na ADF, sun kaddamar da wani babban hari a ranar Lahadi kan wani sansanin soja a birnin Eringeti dake gabashin DRC-Congo.
Majiyar wata kungiyar farar hula dake wurin da aka tuntuba, ta bayyana cewa, wadannan 'yan tawaye sun ci kuma nasarar mamaye wani yanki na birnin Eringeti, dake da nisa kilomita 60 daga birnin Beni, bayan awa guda ana bata kashi.
Gumurzu ya janyo ficewar dimbin mutane daga wurarensu domin kaura zuwa Luna, dake gundumar Ituri, in ji wani mamba na wannan kungiyar farar hula da ya bukaci a sakaya sunansa.
Babu wani adadi da aka samu kan musanyar wuta, ake zaton an ci gaba da gumurzu tsakanin bangarorin biyu har karshen yammacin ranar Lahadi, a cewar majiyoyin dake wurin.
An kafa kungiyar 'yan tawayen ADF a cikin shekarun 1990 a karkashin kungiyoyin dake adawa da shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni. Bayan da rundunar sojojin Uganda ta ci nasara kansu, wadannan 'yan tawaye masu kishin islam sun ci gaba da gudanar da ayyukan a gabashin kasar DRC-Congo. (Maman Ada)