in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fuskantar kalubale a fannin fitar da kayayyaki zuwa ketare
2015-05-06 09:54:30 cri

Wani rahoto da ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ta fitar, ya nuna cewa, kasar na fuskantar kalubale, game da yadda za ta inganta sha'anin fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare, a gabar da ake ci gaba da fuskantar matsalar farfadowar tattalin arzikin kasashen duniya da dama.

Rahoton ya ce, batun tafiyar hawainiya, da tattalin arzikin kasashe da dama ke yi, da kuma manufar rage darajar kudade da wasu kasashe ke aiwatarwa, na cikin dalilan da suka haifar da wannan koma baya. Sauran dalilan sun hada da raguwar bukatun masu sayayya, da ma ci baya a daukacin harkokin cinikayyar kasa da kasa.

A daya hannun kuma, batun takara shi ma ya taka muhimmniyar rawa wajen fadada wannan matsala, inda yayin da manyan kasashe kamar Amurka ke bude sabbin kasuwannin manyan hajoji, a hannu guda kuma wasu kasashe masu tasowa kamar Indiya, su ma na kara bunkasa kasuwanninsu na matsakaitan hajoji.

Bugu da kari rahoton ya nuna cewa, matakin karya darajar kudade da wasu kasashe ke dauka domin inganta sha'anin fidda nasu kayayyakin, da kuma karfafa tattalin arzikinsu, ya sanya kudin kasar ta Sin RMB kara daraja, ta yadda hakan ke shafar takarar da kayayyakin kasar ke yi, da na sauran kasashen duniya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China