Babban jami'i mai ba da shawara ta fuskar siyasa a nan kasar Sin Yu Zhengsheng, ya ce, Sin na fatan karfafa dangantakarta da kasar Algeriya. Mr. Yu wanda ya bayyana hakan yayin zantawarsa da shugaban majalissar kasar Algeria Abdelkader Bensalah a nan birnin Beijing, ya jinjinawa kasar Aljeriya bisa turo Mr. Bensalah da ta yi, domin halartar babban bikin da kasar Sin za ta gudanar a ranar Alhamis.
Yu ya ce, Sin da Algeriya na da tarihi iri daya, game da kokarin da suka yi a baya na dakile mahara daga ketare, da neman 'yancin kai, kana kasashen biyu suna da dadadden tarihi na gargajiya, da burin zaman lafiya wanda suke matukar martabawa. Kaza lika ya jaddada aniyar Sin game da hada gwiwa da Algeria wajen fadada huldar kawance da samun ci gaba tare.
A nasa bangare, Mr. Bensalah, cewa ya yi, yana matukar farin ciki da samun damar halartar taron da Sin za ta gudanar, na cika sherkaru 70 da kawo karshen harin Japan, tare da fatan ziyarar tasa za ta kara yaukaka dankon zumunci tsakanin kasarsa da Sin, tare da kudurin sassan biyu na hada karfi da karfe, wajen wanzar da zaman lafiya da lumana a duniya baki daya. (Saminu)