in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin kunar bakin wake a jihar Bornon Najeriya ya haddasa mutuwar mutane 7
2015-11-23 10:44:32 cri
Rahotanni sun bayyana cewa harin kunar bakin wake da aka kai a birnin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno a jiya Lahadi, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 7, tare da jikkata wasu da dama.

Kafofin yada labarun yankin sun ce da yammacin wannan rana, wata mace 'yar kunar bakin wake ta tada wani bam dake jikin ta, wanda hakan ya haddasa kisa da jikkatar mutane da dama. Daga bisani 'yan sanda sun isa inda wannan lamari ya auku, an kuma garzaya da wadanda harin ya ritsa da su zuwa asibiti domin samun jiyya. Babu dai wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin wannan harin.

Jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya dai na shan fama da hare-haren kungiyar Boko Haram wadda ke da sansani a yankin.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China