in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF ta ce yara 800,000 ke tserewa daga gidajensu a arewa maso gabashin Nigeriya
2015-04-14 10:25:53 cri

Asusun kula da kananan yara na MDD wato UNICEF a cikin rahoton da ya fitar jiya Litinin ya ce, a kalla kananan yara 800,000 ne aka tilasta wa tserewa daga gidajensu sakamakon tashin hankalin da yankin arewa maso gabashin kasar ke fuskanta tsakanin 'yan ta'addan Boko Haram, sojoji da masu aikin kare kai na farar hula.

Rahoton UNICEF mai taken kewar kuruciya, an fitar da shi ne shekara daya bayan da aka sace 'yan matan Chibok dari biyu a jihar ta Borno dake yankin. Wannan rahoto ya nuna adadin yara kananan dake gudun neman tsirar da rayukansu a ciki, da kuma wajen tsallaka kan iyakar kasar zuwa kasashen Kamaru, Chadi,da Nijar.

Sabon rahoton na UNICEF ya bayyana yadda tashin hankalin ya yi mummunan tasiri a kan rayuwan kananan yara a Nigeriya da sauran kasashen. Ban da wadanda aka kashe, aka daddatse wa wassu sassan jiki, da wadanda suka rasa muhallansu, kungiyar ta Boko Haram ta yi amfani da kananan yara a matsayin masu dafa musu abinci, masu taya su kai hare hare da kuma masu kawo musu bayanai, ko duba musu hanya.

A cikin rahoton, an bayyana yadda ake amfani da 'yan mata wajen auren 'yan ta'addan dole, ayyukan karfi dama yi musu fyade, musamman ma yadda ake harin dalibai da malaman makaranta. Fiye da makarantu 300 aka kai wa hari ko aka lalata, sannan a kalla malaman makarantu 196 da dalibai 314 aka hallaka ya zuwa karshen shekarar ta 2014.

A daukin da ta bayar sakamakon wannan rikici, UNICEF ya yi ta ba da agajin jin kai a watanni 6 da suka gabata, ta samar da kwarin gwiwwa na shawarwari da kwantar da hankali ga yara sama da 60,000 da suka fuskanci wannan rikici a Nigeriya, Kamaru, Chadi da Niger. Sannan a yi aiki tare da sauran abokan hadin gwiwwa wajen samar da ruwan sha mai tsabta da kayayyakin jinya, taimakawa maido da tsarin karatu, ta samar da azuzuwan wucin gadi da abinci masu gina jiki ga yara. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China