Kungiyar kula da yara kanana ta MDD (UNICEF) ta nuna damuwarta sosai game da sace sacen kananan yara a kasar Cote d'Ivoire, tare da yin kira ga hukumomin kasar da su sanya wani kokari domin gano masu aikata wannan laifi.
Kungiyar UNICEF ta nuna damuwa sosai kan sace sacen kananan yara da kuma gano gawawwakin mutanen da aka ma azaba, in ji madam Adele Khudr, wakiliyar kungiyar UNICEF a kasar Cote d'Ivoire a cikin wata sanarwar a ranar Litinin.
A cewar jami'an 'yan sandan Cote d'Ivoire, a kalla kananan yara 21 aka sace tun cikin watan Disamban da ya gabata a dukkan fadin kasar, kuma yawancin gawawwakin da ake ganowa suna dauke da alamun azabatarwa. A cewar shugabar kungiyar UNICEF, ayyuka ne da ba za'a rufe idanu kansu ba, kuma sun kasance manyan laifuffukan keta hakkin yara ne. Ya kamata hukumomin Cote d'Ivoire su yi duk aikin gano cikin gaggawa mutanen dake aikata wadannan manyan laifuffuka domin amsa laifinsu gaban kotu, in ji madam Adele Khudr.
Haka kuma, UNICEF ta yi kira ga gwamnatin kasar da ta dauki duk wasu matakan da suka dace na fadakar da al'ummomin kasar, har ma da yara, domin rage hadura da kuma karfafa matakin kasa na rigakafi da bincike a lokacin da aka samu bace bacen kananan yara. (Maman Ada)