Gwamnatocin kasashen Sin da Kenya sun sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi 3 kan wasu ayyukan tallafi a kasar Kenya, wacce ke gabashin Afrika.
Ayyukan 3 wadanda aka ware kudi kimanin dalar Amurka miliyan 152.4 kuma an sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Larabar nan a Nairobi, tsakanin sakataren ma'aikatar adana kudaden kasar Kenya Henry Rotich, da ministan kasuwancin kasar Sin Gao Hucheng.
A yayin bikin sanya hannun, shugaba Kenyatta, ya bayyana bukatar hadin kan Sin da Kenya domin sanya ido kan yadda za'a aiwatar da ayyukan raya ci gaban Afrika, wanda aka ambata a yayin taron hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC.
A nasa bangaren, Gao Hucheng ya ce, bayan tallafawa Kenya a fannin makamashi da kayayyakin more rayuwa da aikin gona da ilmi da lafiya, haka zalika kasar Sin, tana tallafawa Kenya wajen ci gaban fannin gandun daji.(Ahmad Fagam)