in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Kenya ya yabawa Sin wajen tallafawa shirin kula da namun daji
2015-11-11 10:08:19 cri

Wani jami'in kasar Kenya ya bayyana cewar, taimakon da kasar Sin ke baiwa bangaren kare namun daji yana matukar taimakawa wajen yaki da masu hallaka namun daji a kasar ta Kenya.

Daraktan kula da sashen gandun daji na ma'aikatar kare muhalli da albarkatun kasa na Kenya Stephen Manegene, ya shedawa tawagar ma'aikatan kula da gandun daji na kasar Sin cewar, kyakkyawar dangantakar dake wanzuwa tsakanin kasashen biyu, ya saukaka hanyoyin da ake bi wajen yaki da masu farautar giwa da karkanta.

Manegene, ya kara da cewa, Kenya ta karbi taimako mai yawa daga gwamnatin kasar Sin da ma sauran hukumomi masu zaman kansu, domin amfani da su a fannin kula da namun daji. Kuma a shekaru 4 da suka gabata, Kenya ta karbi bakuncin wasu manyan tawagogi 3 wadanda suka ziyarci kasar domin tattauna yadda za'a magance batun kashe namun daji da dakile aniyar masu safarar hauren giwa a kasar.

Daraktan ya ce, matakin da za'a dauka na gaba shi ne, tsara takardun yarjejeniya da nufin hada gwiwa da kasar Sin don ci gaba da lura da batun da ya shafi kula da lafiyar namun dajin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China