Wani jami'in Kenya ya tabbatar da cewar, shirin hadin gwiwar kasar Sin da Kenya a fannin aikin gona, da kiwon dabbobi da kiwon kifi, ya yi matukar samun bunkasuwa, a sakamakon aiwatar da shirin, an cimma burin bunkasa samar da abinci da kudin shiga ga mazauna yankuann karkara.
Da yake jawabi a yayin taron hadin gwiwar kasar Sin da Kenya a fannin aikin gona a Nairobi, ministan kula da aikin gona na Kenya Adan Mohamed, ya ce, taimakon da kasar Sin ke bayarwa yana da muhimmanci sosai wajen habaka ci gaban aikin gona na Kenya, wanda shi ne kashin bayan tattalin arzikin kasar.
Mohamed, ya kara da cewar, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Kenya a fannin aikin gona tana samun gagarumin ci gaba, musamman ma wajen yin bincike, da ba da horo, da kuma musayar fasahar zamani.
Jami'an kasar ta Kenya sun gana da tawagar kasar Sin mai mutane 45, inda suka tattauna muhimman al'amurran kan batun gona da kiwon dabbobi da kifi.
Mohamed ya ce, yadda kasar Sin ke saurin bunkasuwa a fannin aikin gona irin na zamani, hakan yana matukar tallafawa ci gaban kasashe masu tasowa, ya kara da cewar, Kenya za ta hada kai da kasar Sin a bangaren noman rani da kuma sarrafa kayayyakin amfanin gona da ake nomawa a cikin kasar.
Zhao Weining, mataimakin daraktan sashen hulda da kasashen duniya a ma'aikatar aikin gona ta kasar Sin ya ce, Sin a shirye take ta hada gwiwa da kasar Kenya don habaka fannin aikin gona a kasar.(Ahmad Fagam)