Wani babban jami'in kasar Kenya ya fada a Talatar nan cewar, yadda masana'antun kasar Sin suka samu bunkasuwa a cikin shekaru 20 da suka gabata, wata alama ce dake kara kaimi ga kasashen yankin dake kudu da hamadar Sahara wajen sauya fasalin noma daga tsarin da ake amfani da shi a da zuwa na zamani.
Wilson Songa, wanda shi ne babban sakatare a ma'aikatar ci gaban masana'antu da ci gaban sana'o'i na kasar ya ce, Kenya za ta yi amfani da irin darrusan da ta koya daga kasar Sin wajen sauya fasalin tsarin aikin gonarta domin mayar da shi na zamani.
Songa ya ce, kasar Sin ta koyar da su dabaru wadanda za su iya kawo sauyi ga sha'anin aikin gona na kasar.
Jami'in na daya daga cikin tawagar wakilan da gwamntain Kenya ta tura kasar Sin domin karo ilmi kan sauya tsarin masana'antu a tsakiyar watan Satumba.
Ma'aikatar ciniki ta kasar Sin ta dauki nauyin shirya taron bitar na tsawon mako guda ga jami'an na kasar Kenya domin ilmantar da su sabbin dabarun raya tattalin arziki da kasar Sin ke amfani da shi.
Songa, ya sheda wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a birnin Nairobi na kasar Kenyan cewar, tuni gwamnatin kasar ta fara tuntubar hukumar da ke kula da sha'anin sauye sauye ta kasar Sin domin kulla yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin raya tattalin arziki.(Ahmad Fagam)