in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban UNHCR na shirin kai ziyara Kenya
2015-05-05 10:01:41 cri

A yau ne ake sa ran babban kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR Antonio Guterres zai kai ziyara kasar Kenya don tattaunawa da gwamnatin kasar game da shirin da ake na kwashe sama da 'yan gudun hijirar kasar Somaliya 350,000 da ke zaune da sansanonin 'yan gudun hijirar kasar.

Guterres wanda zai ziyarci kasar ta Kenya daga ranar 5 zuwa 8 ga watan Mayu, zai kuma tattauna da jami'an gwamnatin kasar da hukumomin bayar da agaji, inda za su mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi 'yan gudun hijira.

A shekarar 2013 ne kasashen Kenya da Somaliya da UNHCR suka sanya hannu kan yarjejeniyar kwashe 'yan gudun hijirar wadda za a aiwatar cikin tsawon shekaru uku.

Bayanai na nuna cewa, kasar Kenya ta shafe shekaru da dama tana karbar dubban 'yan gudun hijirar Somaliya da ke gujewa fadan da ake gwabzawa a yankin tsakiya da kudancin Somaliya, lamarin da ya cusa rayuwar wadannan mutane cikin hadari, hakan ya sa al'ummomin kasa da kasa neman matakan ba su kariya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China