in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi maraba da yarjejeniyar da aka cimma game da Libya
2015-12-18 09:29:13 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya bayyana farin cikin sa, game da sanya hannu da sassan Libya suka yi kan yarjejeniyar siyasa a kasar.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, Mr. Ban ya yi fatan yarjejeniyar za ta dora Libya kan turbar sake ginin kasa bisa doron dimokaradiyya, tare da mutunta dokokin kasa da hakkokin bil'adama. Kaza lika sanarwar ta kara da cewa, yarjejeniyar za ta ba da damar kafa gwamnati guda mai kunshe da wakilcin dukkanin bangarori.

Ban Ki-moon ya taya al'ummar Libya murnar cimma wannan nasara, tare da bayyana aniyar MDD, ta ci gaba da hadin gwiwa da sassan kasar, da goyon bayan mahukuntan kasar, domin tabbatar da wanzuwar yanayin zaman lafiya mai dorewa.

Bugu da kari, Mr. Ban ya yi fatan kulla wannan yarjejeniya zai share fagen kafa gwamnatin rikon kwarya cikin hanzari, da kuma kaddamar da hukumominta a birnin Tripoli, fadar mulkin kasar.

Ya ce, akwai jan aiki gaban al'ummar kasar Libya, amma duk da haka ya yi fatan za su ci gaba da marawa gwamnatinsu baya, har a kai ga cimma burin da aka sanya gaba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China