in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya kara wa'adin UNSMIL a Libya
2015-09-11 10:55:34 cri

A ranar Alhamis din nan ne kwamitin tsaro na MDD ya zartas da kudurin kara wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya a kasar Libya UNSMIL zuwa ranar 15 ga watan Maris na shekarar 2016.

Kwamitin ya yabawa UNSMIL da wakilin musamman na babban sakataren MDD dake kasar ta Libya bisa irin kokarin da suka nuna wajen warware rikin siyasar da ya dabaibaye kasar.

A hannu guda kuma, MDD ta bukaci UNSMIL da ta mai da hankali wajen daukar matakan da za su tabbatar da warware rikicin siyasar kasar, musammna ta hanyar gabatar da shawarwari da za su ba da damar zama a tebirin sulhu don tattaunawa da nufin kafa gwamnatin hadaka.

Ka zalika kwamitin tsaron MDD ya bayyana takaicinsa sakamakon samun karuwar hasarar rayukan bakin haure wadanda suka yi yunkurin haurawa kasashen Turai ta gabar tekun Meditareniya, musamman ta gabar tekun dake Libya.

An yi garambawul ga shirin na UNSMIL a watan Maris bisa tanade tanaden dokokin kwamitin tsaro na MDD da nufin warware rikicin siyasar kasar ta Libya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China