in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi na'am da shirin sasanta rikicin siyasar Libya
2015-07-17 09:54:43 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya yi maraba da shirin yarjejeniyar sasanta rikicin siyasar kasar Libya da galibin wakilan kasar suka cimma ranar 11 ga watan Yuli a garin Skhirat da ke kasar Morocco.

Wata sanarwa da kwamitin sulhun ya fitar ta nuna cewa, wasu daga cikin sassan da ke fada da juna a kasar sun amince da wannan yarjejeniya da MDD ta jagoranta, duk da cewa babbar kungiyar wakilan kasar ta GNC ba ta halarci ganawar ba.

Mambobin kwamitin sulhun sun kuma yaba da namijin kokarin jagororin da suka shirya daftarin yarjejeniyar da aka tsara da nufin warware rikicin harkokin mulki da na tsaron kasar.

Sun kuma yi kira ga dukkan bangarorin kasar da su shiga a dama da su a tattaunawar siyasar kasar, kana su goyi bayan yarjejeniyar da ake fatan za ta ciyar da shirin mika mulkin kasar gaba, musamman ta hanyar kafa gwamnatin hadaka

Mambobin kwamitin sulhun MDDr sun kuma godewa masarautar kasar Morocco da kasashen Aljeriya, da Masar, da Tunisia, da sauran abokan hulda saboda rawar da suka taka na ganin an cimma wannan yarjejeniya.

Kasar Libya dai ta tsinci kanta cikin tashin hankalin siyasa ne, tun bayan da boren siyasar kasar na shekarar 2011 da ya yi awon gaba da tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi, lamarin da ya haifar da kungiyoyin masu tayar da kayar baya a kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China