in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon manzon MDD mai kula da batun Libya ya kama aiki
2015-11-18 09:32:40 cri

Wakilin musamman na babban magatakardan MDD mai kula da batun Libya Martin Kobler ya bayyana kudurin sa na yin aiki da dukkan bangarorin kasar, a kokarin da ake na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Kakakin MDD Stephane Dujarric wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai jim kadan da fara aikin sabon jami'in, ya kuma bukaci dukkan masu ruwa da tsaki a kasar ta Libya da su hau teburin sulhu

Jami'in na MDD ya kuma zayyana tsarin ayyukansa, wadanda suka hada da ganawa da bangarorin 'yan siyasa da sauran abokan huldar kasar da nufin warware ragowar batutuwan da ke kan teburi.

Bugu da kari, Mr Kobler na fatan tattaunawa da masu fada a ji na kasar game da batutuwan da suka shafi tsaro.

Kafin nada shi kan wannan mukami, Mr Kobler ya rike mukamin wakilin babban magatakardan MDD na musamman, kana shugaban tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar demokiradiyar Congo.

A farkon watan Oktoba ne dai MDD ta ba da shawarar kafa gwamnatin hadaka a kasar ta Libya, da nufin kawo karshen rikicin da kasar ta fada tun bayan boren siyasar da ya kifar da gwamnatin Muammar Gaddafi a shekarar 2011.(Yaya Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China