in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kuri'ar raba gardama ya yi nasara ga yawanci a CAR, in ji jami'in MDD
2015-12-15 09:30:19 cri

Wani babban jami'in MDD a ranar Litinin din nan ya ce, an aiwatar da kuri'ar raba gardama cikin nasara a yawancin yankunan kasar jamhuriyar demkradiya ta Kongo CAR, duk da wassu rahotanni na 'yan abin da ba a kan rasa da firgita masu zaben da ma jami'an zabe.

Karamin magatakardar MDD a kan ayyukan samar da zaman lafiya, Herve Ladsous ya furta hakan da yake bayanin a gaban kwamitin tsaron majalissar game da yanayin da ake ciki a kasar ta CAR.

Ya kuma ce, ma'aikatan wanzar da zaman lafiya biyu sun samu rauni a rikicin da ya auku a Bangui da Bria, yana mai bayanin cewa, ayyukan 'yan kalilan bai kamata ya ruguza fata da burin yawancin zabukan da aka gudanar cikin nasara ba.

Mr Ladsous ya yaba wa rajistan kusan masu kada kuri'a miliyan biyu, wadanda ke wakiltan kashi 95% na adadin wadanda suka cancanci zaben, wanda ya bayyana karfin niyya na ganin sauyi da al'umma ke da shi.

Jami'in na MDD ya ce, yana da muhimmanci ga 'yan kasar ko da a cikin gida ko ma a wajen, su iya kada kuri'a da za su zabi gwamnatinsu mai zuwa ba tare da fuskantar wata tsangwama ba.

Mr Ladsous daga nan sai ya ce, tawagar MDD a kasar wato MINUSCA da sauran rassan majalissar za su ci gaba da ba da gudunmuwarsu ta fasahohi, kayayyakin aiki, da tsaro don a samu ganin gwamnatin rikon kwaryan ta cimma bukatarta.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China