in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzan MDD ya ce tattaunawa ne kadai mafita rikici a CAR
2015-10-29 10:47:04 cri

Sakamakon rikicin da ke ta wanzuwa a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR tun farkon wannan makon, manzon musamman na MDD ya ce, tattaunawa ne kadai mafita a cikin wannan lamari.

Ofishin MDD a jamhuriyar Afrikan ta Tsakiya MINUSCA ya tabbatar da cewa, an raunata wani ma'aikacin wanzar da zaman lafiya a lokacin rikicin da ake zargin 'yan kungiyar anti-Balaka ne suka aikata a kan tawagar ta MINUSCA a kan hanyarsu ta isar da kayayyaki daga kan iyakan kasar Kamaru zuwa Bangui a ranar Talata, kamar yadda kakakin majalissar Stephane Dujarric ya yi bayanin cikin sanarwar da ya fitar.

A sanarwar da aka fitar wa manema labarai, an kuma bayyana cewa, an sake kai wa wata tawagar ta MINUSCA hari kan wannan hanyar a Larabar da ta gabata, sai dai babu wanda ya jikkata.

Wakilin musamman na magatakardar MDD a kasar Parfait Onanga-Anyanga a cikin wata sanarwa ya yi kira ga daukacin 'yan kasar da su kai zuciya nesa su kuma guje wa kara rura wutar rikici da zai haifar da mummunan sakamako.

Haka kuma manzon ya soki amfani da tashin hankali wajen warware matsalar da ake fuskanta, yana mai cewa, abubuwan dake faruwa kwanakin nan bai kamata su kai ga yawaita asarar rayuka ba, kuma wani koma baya ne ga samar da zaman lafiya.

Onanga-Anyanga ya ce, tashin hankali ba zai taba kawo mafita ba. Tattaunawa kadai ne mafita da kasar ya kamata ta runguma.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China