in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya soki kisan ma'aikacin wanzar da zaman lafiya a CAR
2015-11-11 13:21:55 cri

Magatakardar MDD Ban Ki-moon ya soki kisan da aka yi wa ma'aikacin wanzar da zaman lafiya a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR a jiya Talata, tare da bukatar a binciko a kuma gurfanar da wadanda ke da hannu a gaban shari'a.

Magatakardar ya soki kisan ne na ma'aikacin dake aiki a ofishin majalissar ta MINUSCA, a garin Batangafo mai tazaran kilomita 400 daga arewacin Bangui, babban birnin kasar, in ji sanarwar da kakakinsa ya fitar wa manema labarai.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China