in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da a yi zabe cikin adalci da gaskiya a CAR
2015-10-21 09:43:02 cri

Bayan nuna juyayi da takaici a kan tashin hankalin da ake fuskanta tare da rashin daidaito a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR, a ranar Talatan nan, kwamitin tsaron MDD ya jaddada muhimmancin ganin an aiwatar da zabubukan kasar cikin adalci da kuma sauraran bukatar kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasar cikin gaskiya nan da karshen wannan shekara ta 2015.

A cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin ya bayar, ya ce, kwamitin da kakkausar murya ya soki tashin hankalin da ya barke tare da harin da aka kai wa fararen hula, fada tsakanin kabilu, da cin zarafi musamman da aka yi a kan mata da yara, satar kayayyakin jama'a, da kuma hari a kan ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar.

Kwamitin har ila yau ya jaddada cewa, wadansu hare haren za su iya kasance laifukan yaki, kuma wadanda ke da hannu a ciki sun aikata ayyukan keta dokar jin kai ta kasa da kasa, da cin zarafin dan adam, dole su dauki alhaki a kan su.

Kwamitin ya jaddada goyon bayan shi a kan mahunkuntar gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin Catherine Samba-Panza, sannan ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da su mai da hankali a kan duk abin da zai kawo zaman lafiya da sulhunta juna ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu a taron Bangui a watan Mayun wannan shekara.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China