in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta mika jami'ar koyon aikin jiyya da ta gina ga Ghana
2015-09-21 10:49:54 cri

A kwanakin baya ne aka gudanar da bikin mika jami'ar koyan aikin jiyya da gwamnatin kasar Sin ta aiwatar a kasar Ghana, inda aka damka ta ga ma'aikatar ilmi ta Ghanan. A madadin gwamnatocin kasashen biyu, jakadar Sin a Ghana Sun Baohong da Ministar ba da ilmi ta Ghana Naana Jane Opoku-Agyemang sun sa hannu kan takardar mika aikin.

Yayin bikin, Sun Baohong ta yi jawabi, inda ta bayyana cewa, aikin gina jami'ar koyon aikin jiyya da kamfanin Sin ya yi a Ghana alama ce da ke nuna aminci tsakanin al'ummar kasashen biyu, sannan ta ce, tana fatan jami'ar za ta baiwa daliban kasar Ghana damar koyon ilmin a fannin kiwon lafiya, ta kara da cewa, a kullum kasashen Sin da Ghana sun fi mai da hankali ne wajen hadin gwiwarsu a fannin samar da ilmi, kuma tuni an fara samun sakamako mai kyau.

A nata jawabin, Opoku-Agyemang ta nuna matukar godiya ga irin taimakon da gwamnatin Sin ke baiwa kasar Ghana, sannan ta bayyana cewar, gwamnatin kasar a shirye take ta kara karfafa hadin gwiwa tsakaninta da gwamnatin Sin domin kara inganta fannin ilmin Ghana yadda ya kamata.

Kasar ta Sin ta gina jami'ar ne a birnin Ho na jihar Volta a kasar Ghana.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China