Dubun dubatar al'ummar kasar Tanzaniya sun yi fitar dango domin kada kuri'unsu a zaben shugaban kasar, da na majalisun dokoki, da kuma na wakilan shiyyoyi a jiya Lahadi, kuma shi ne zabe mafi zafi da kasar ta taba fuskanta tun bayan samun 'yancin kanta a shekarar 1961.
Jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi wato CCM, wacce ta shafe sama da shekaru 50 tana mulkin kasar, na fuskatar zazzafar adawa daga gamayyar jam'iyyun adawar kasar 4 da suka dunkule karkashin jam'iyyar Chama Cha Demokrasia na Maendeleo wato CHADEMA domin kalubalantar jam'iyyar mai mulki a zaben.
Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar CCM John Magufuli, kuma ministan ayyuka a gwamnatin shugaba Jakaya Kikwete, wanda zai kammala wa'adin mulkinsa karo na 2 na tsawon shekaru biyar, sun fafata ne da 'dan takara na jam'iyyar CHADEMA kuma tsohon firaiministan kasar Edward Lowassa.
Jam'iyyun Civic United Front (CUF), da National League for Democracy da kuma NCCR-Mageuzi ne suka dunkule da wuri guda don mara baya ga jam'iyyar CHADEMA a zaben.
Shi dai Lowassa, ya sauya sheka ne daga jam'iyyar CCM a watan Yuli, bayan da jam'iyyar ta hana shi takarar shugabancin kasar, inda ta baiwa abokin hamayyarsa Magufuli.
Sama da mutane miliyan 22 suka fito don kada kuri'unsu a babban zaben kasar, wacce ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a gabashin Afrika in baya ga kasar Kenya.(Ahmad Fagam)