Hukumar da ke sanya ido kan kamfanonin sadarwa a Najeriya, ta ce ta rage tarar dala biliyan 5.2 da ta ci kamfanin sadarwa na MTN.
Kamfanin na MTN ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya cewa, hukumar ta rage tarar ce bayan wasu tattaunawa da hukumomin kasar.
Hukumomin Najeriyar dai sun ci kamfanin na MTN tarar ce, saboda ya gaza rufe layuka miliyan 5.1 a watannin Agusta da Satumba saboda ba su da rijista.
Yanzu dai kamfanin na MTN zai biya tarar dala biliyan 3.4 ne kafin ranar 31 ga watan Disamba(Ibrahim)