Mataimakin shugaban kwamitin kungiyar AU Erastus Mwencha, ya bayyana a yayin ganawa da manema labari a kwanan baya cewar, kasashen Afrika sun kasance matakin farko wajen raya masana'antu, lamarin da ya haifarwa kasar Sin samun sakamako mai kyau a wannan fanni, kamata ya yi kasashen Afrika su koyi fasahohin da Sin ta samu wajen neman bunkasuwa, saboda haka tabbatar da hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu a dai dai lokacin da ake bukatar hakan.
Erastus ya ce, a shekarun baya, kasar Sin da kasashen Afrika suna yin musayar ra'ayoyi da hadin gwiwa a fannonin al'adu da siyasa, Sin ta kasance babbar abokiyar huldar cinikayya ga kasashen Afrika, bangarorin biyu suna da makoma mai kyau wajen yin hadin gwiwa a fannonin cinikayya da zuba jari da aikin gona da samar da muhimman ababen more rayuwa.
Bugu da kari, Erastus ya bayyana cewa, dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika wani muhimmin dandali ne, wajen musayar ra'ayoyi da hadin gwiwa a tsakaninsu. A karo na farko za a gudanar da taron koli na dandalin tattaunawa din a nahiyar ta Afrika, kungiyar AU tana kokari sosai wajen shirya taron cikin himma da kwazo, domin mai da wannan taron kolin da za a shirya a Johannesburg a matsayin wani dandalin inganta hakikanin hadin kai a tsakanin bangarorin biyu.(Lami)