in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen Afrika da su gaggauta bunkasa kimiyya da fasaha
2015-12-03 10:46:10 cri

An bukaci gwamnatocin kasashen Afrika a ranar Laraba da su yi hadin gwiwa ta hanyar wani tsarin shawarwari na shiyya domin bunkasa kimiyya da fasaha da kuma kirkire kirkire a nahiyar Afrika.

Sakataren kasar Kenya a fannin ilimi, Fred Matiangi, ya bayyana cewa, irin wadannan shawarwari za su taimaka wajen bullo da wata manufar siyasa domin tallafawa ci gaba da sauye sauye a Afrika, tare da tabbatar da 'yancin nahiyar da kuma samar da damammaki ga matasa na gaba.

Shugabannin gwamnatoci ya kamata su fara nuna fifiko wajen kirkirowa domin yin amfani da takaitattun albarkatunsu, in ji mista Matiangi a yayin wani zaman taron shawarwari na manyan kwararru (SED) kan kimiyya da fasaha da kuma kirkire kirkire a birnin Nairobi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China